Kamfanin mai na kasa NNPC ya bayyana cewa zai dakatar da shigo da tataccen man fetur daga Kasashen ketare a watan Disamban shekarar 2024 mai zuwa.

 

Kamfanin ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar 23 ga watan Nuwamba.

 

Kamfanin ya kara da cewa matatun man za su fara aiki ne kafin lokacin da aka sanya.

 

Shugaban kamfanin Mele Kyari ne ya tabbatar da hakan a lokacin da yake ganawa da masu ruwa da tsaki a bangaren man fetur a Najeriya.

 

Kamfanin ya kara da cewa ana sa ran matatar man garin Port-Horcourt za ta fara aiki ne a watan Janairun sabuwar shekara da Warri, bayan kammala gyaran matatar a karshen shekarar da muke ciki.

 

NNPC ya ce zuwa kuma karshen shekarar 2024 matatar man Fetur ta Kaduna za ta fara aiki, wanda hakan zai sanya a dakatar da shigo da mai daga kasashen ketare.

 

Kamfanin na NNPC ya kuma yi hasashen samun ribar naira Tiriliyan 4.5 zuwa karshen shekarar 2023 da muke ciki.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: