Wani mummunan hatsarin mota ya yi ajalin mutane 12 da jikkata wasu fiye da 30 a jihar Plateau.

Lamarin ya faru ne a jiya Alhamis 14 ga watan Disamba a yankin Hawan-Kibo da ke karamar hukumar Riyom a jihar.
Jaridar Punch ta tababar da cewa motar tirela ce makare da hatsi da kuma mutane ta kife yayin da ta ke haurawa a hanyar lokacin da abin ya afku.

Wani shaidar gani da ido ya ce bayan motar ta kife dukkan hatsin ya zube a ramuka tare da barin mutane matattu nan take.

Kwamandan hukumar FRSC a jihar, Mista Godwin Alphonsus ya tabbatar da faruwar lamarin a jiya Alhamis 14 ga watan Disamba a Jos.
FRSC ta ce hatsarin ya afku ne da tsakar rana a jiya Alhamis inda tirelar ta kife a cikin rami yayin da take haura hawan titin.
Sun kara da cewa take su ka dauki mutane fiye da 30 da su ka jikkata zuwa asibiti mafi kusa don ba su kulawa ta musamman .