Zanga-zanga ta ɓarke bayan da kotun ƙoli a Abuja ta yanke hukuncin a kan zaɓen gwamnan jihar Nassarawa.

An toshe hanyar zuwa Jos daga Lafia bayan da kotun ta yanke hukuncin yau Juma’a.

Kotun ta ayyana Abdullahi Sule na jam’iyyar APC a matsayin halastaccen gwamnan jihar.

Masu zanga-zangar sun kona tayoyi a babbar hanyar lamarin da ya hana matafiya wucewa.

Sai dai rahotanni sun ce jami’an tsaro sun yi ƙoƙarin kai ɗauki lamarin da ya sa zanga-zangar ta lafa.

Idan ba a manta ba kotu a baya ta soke nasarar gwamna Abdullahi Sule na jam’iyyar APC a wanda hukumar zaɓe ta ayyana a matsayin wanda yayi nasara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: