Kungiyar Dattawan Arewa ACF ta soki shirin dauke hedkwatar FAAN daga birnin tarayya Abuja zuwa Jihar Legas.

 

Sannan ƙungiyar ba kuma ta goyan bayan dauke wasu manyan ofisoshin babban bankin Kasa na CBN daga Birnin zuwa Jihar ta Legas.

 

Kungiyar ta kara da cewa yin hakan ka iya maida yankin Arewa a matsayin saniyar ware.

 

Sakataren yada labaran kungiyar na Kasa Farfesa Tukur Muhammad Baba shine ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.

 

Tukur ya kara da cewa maida wasu ofisoshin Jihar Legas, hakan ka iya cutar da ‘yan Arewa.

 

Sannan kungiyar ta zargi wasu manyan Jami’an gwamnatin da nakasa Arewa da sauran bangarorin Kasar.

 

Kungiyar ta kuma yi Alla-wadai da wannan mataki na maida Arewacin Kasar Saniyar ware.

Leave a Reply

%d bloggers like this: