Akalla mutane 16 ne suka rasa rayukansu hudu suka jikkata a wani hadarin mota da ya afku a cikin karamar hukumar Makarfi da ke Jihar Kaduna.

Hadarin ya faru ne a ranar Lahadi a kwanar Taban Sani a Tashar Yari da ke kan hanyar Kano zuwa Kaduna.


Kuma ya rutsa ne da wata mota kirar Bas wadda ta taso daga Jihar Kano zuwa Jihar Benue.
A cikin wata sanarwa da kwamandan hukumar kiyaye afkuwar hadaurra FRSC ta Jihar Kaduna Kabir Nadabo ya fitar, ya ce hadarin ya faru ne sakamakon gudun wuce sa’a da direban ke yi wanda hakan ya sanya motar ta kwace tare da fadawa rami.
Nadabo ya ce bayan faruwar Lamarin mutane hudun da suka jikkata an mikasu zuwa Asibitin garin Makarfi da ke Jihar domin kula Lafiyarsu.
Inda kuma aka ajiye gawarwakin wadanda suka rasa rayukansu a Asibitin Shika da ke cikin garin Zariya.