Gwamnatin Jihar Filato ta sanya dokar hana fita na tsawon a wanni 24 a Jihar.

 

Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin Jihar Gyang Bere ya fitar a yau Talata.

 

Sakataren ya ce daukar matakin ya zama dole duba ga yadda rashin tsaro ke kara karuwa a fadin Jihar.

 

Sannan sanarwar ta bayyana cewa dokar za ta shafi karamar hukumar Mangu ta Jihar wadda ta ke fama da yawaitar hare-haren ‘yan bindiga da garkuwa da mutane.

 

Jihar Filato na ɗaya daga cikin Jihohin Najeriya da ke fama da yawaitar hare-haren ‘yan ta’adda,inda suke hallaka mutane kashe su da kuma garkuwa dasu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: