Hukumar ya ki da masu yiwa tattalin arzikin Kasa zagon kasa ta EFCC ta bayyana cewa a gobe Laraba za ta gurfanar da tsohon gwamnan Jihar Anambra Willie Obiano a gaban babbr kotu da ke Abuja.

Hukumar ta bayyana cewa za ta gurfanar da tsohon gwamnan ne bisa zarginsa da aikata almundahanar naira biliyan Hudu.


Jaridar Punch ta rawaito cewa hukumar za ta gurfanar da tsohon gwamnan ne bisa zarginsa da aikata Laifuka tara.
Babban lauyan hukumar ta EFCC Slyvanus Tahir SAN ne zai jagoranci karin wasu lauyoyi Takwas a yayin shari’ar.
Tsohon gwamnan na daya daga cikin gwamnan da hukumar ta EFCC za ta fara bincike akan badakalar wasu kudade da sauran tuhume-tuhume da ta ke yi musu.