Tsohon gwamnan Jihar Anambra Willie Obiano ya isa babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja, bayan hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta gurfanar da shi.

 

Tsohon gwamnan na Anambra ya isa kotun ne a yau Laraba, bisa rakiyar jami’an hukumar ta EFCC kan tuhumar sama da fadi da naira biliyan hudu da kuma karin wasu zarge-zarge Tara da ake yi masa.

 

EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan mai shekaru 68 ne a gaban mai shari’a Inyang Ekwo.

 

Sai dai bayan karanto masa kunshin zarge-zargen da ake yi masa ya musanta dukkan tuhume-tuhuman da ake yi masa.

 

Bayan musanta zarge-zargen, Lauyan hukumar ta EFCC ya bukaci da kotun ta bayar da umarnin ci gaba da tsare shi a hannun hukumar.

 

Daga karshe kuma an bayar da belin tsohon gwamnan da sharadin gabatar da masu tsaya masa.

 

Daga kuma cikin masu tsaya masa akwai daraktoci biyu da ke aikin gwamnati wadanda suka mallaki filaye a Abuja.

Leave a Reply

%d bloggers like this: