Rundunar ‘yan sandan Jihar Gombe sun samu nasarar kama wasu mata 16 da ake zarginsu da safarar yara a Jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Jihar ASP Mahid Mu’azu Abubakar ne ya bayyana kama wadanda ake zargin.


Kakakin ya ce jagorar mutanen an kamata ne a unguwar Barunde da ke Jihar.
Mahid ya bayyana cewa sun kama mutanen ne bayan mazauna unguwar ta Barunde sun shaida musu yadda matar ta ke tara ‘yan mata a gidan, inda ake yin lalata dasu harta kai ga an yi musu ciki.
Kakakin ya kara da cewa bayan yariya ta haihu matar ta na karbe jariran ta sallami wadda ta haihun.
Kakakin ya ce suna ci gaba da gudanar da bincike tare da ganin an tabbatar da an hukunta matar akan abinda take aikatawa.