Rundunar ‘yan sanda ta Najeriya ta zargi wasu sojojin kasar da hallaka jami’anta uku tare da raunata wasu bayan da sojojin suka bude wa wata tawagar ‘yan sandan wuta a jihar Taraba.

Lamarin ya faru ne a kan hanyar Ibi zuwa Jalingo, kamar yanda wata sanarwa da ‘yan sandan suka fitar ta bayyana cewa tawagar ta masu kai daukin gaggawa ce ta Intelligence Response Team (IRT).

Sanarwar ta ce tawagar tana karkashin jagorancin Felix Adolije, mataimakin sufuritanda na ‘yansanda, inda ta je jihar domin kama wani da ake kira Alhaji Hamisu, wanda ake zargi da cewa kasurgumin mai satar mutane ne.

Daga nan ne sai kawai wasu “sojoji na Najeriyar suka bude wa tawagar wuta ba kakkautawa, lamarin da ya sa sojojin suka kubutar da wanda ake zargin inda ya tsere har yanzu ba a san inda yake ba, a cewar kakakin ‘yan sandan na kasa, Frank Mba.

Amma kakakin sojin Kanar Sagir Musa ya musanta zargin na ‘yan sanda, yana mai cewa sun yi ba-ta-kashi ne da masu satar mutane.

Sanarwar ‘yan sandan ta kara da cewa jami’an ‘yan sandan sun kama mutumin ne za su kai shi hedikwatar ‘yan sanda ta jihar a Jalingo lokacin da sojojin suka bude musu wuta, duk kuwa da cikakkiyar shedar da ke nuna cewa suna kan aikinsu.

Bayan ‘yan sandan, lamarin ya kuma rutsa da ran wani farar hula, da sufeto da kuma wasu ‘yan sandan biyu masu mukamin saja, yayin da wasu ‘yan sandan kuma da ba a bayyana yawansu ba suka samu raunuka.

Sai dai rundunar sojin ta bakin mai magana da yawunta kanar Sagir Musa, ta musanta zargin, tana mai cewa ta yi tsammanin ‘yan sandan tawaga ce ta masu satar mutane domin wasu mutane ne daga yankin sun nemi ta kai musu dauki saboda masu satar jama’a sun kai musu hari.

A dalilin haka ne suka “tsayar da mutanen da ke tafiya a wata motar Bas amma suka ki tsayawa, dalilin da ya sa suka bude musu wuta domin kubutar da mutanen da ake zargin an sace”.

“Sai daga baya ne daya daga cikin wadanda suka tsira ya shaida mana cewa su ‘yan sanda ne daga Abuja, kuma an turo su ne domin gudanar da wani aiki na musamman kan masu satar mutane”.

Sojojin sun ce ‘yan sandan ba su sanar da su cewa za su gudanar da wannan aiki ba, kuma rundunar ‘yan sandan ta jihar Taraba ta ce ba ta san da zuwansu ba.

‘Yan sandan suna zargin mutumin, Alhaji Hamisu da kasancewa kasurgumin mai satar mutane, da suka dade suna nema saboda hannu a sace-sacen jama, ciki har na sace wani dan kasuwa mai harkar mai da aka yi kwanan nan a jihar ta Taraba.

Dan kasuwar mai sayar da mai wanda ba a bayyana sunansa ba a sanarwar, an ce sai da ya biya naira miliyan 100 aka sako shi.

Tuni aka tura wani mataimakin sufeto-janar na ‘yan sanda domin tsara yadda za a yi wa wadanda aka jikkata magani, yayin da kuma aka ajiye gawarwakin wadanda suka mutu a asibiti.

Shugaban rundunar ‘yan sanda ta kasa Muhammad Adamu ya bayar da umarnin gudanar da binciken gaggawa kan lamarin, in ji kakakin rundunar ta kasa Mista Frank Mba, mai mukamin mataimakin kwaminishinan ‘yan sanda.

Sai dai su ma sojoji ta bakin mai magana da yawunsu Kanar Sagir Musa ya ce suna kiran da a kafa kwamitin bincike na hadin gwiwa karkashin jagorancin ‘yan sandan domin tabbatar da gaskiyar abin da ya faru.

Ba dai wannan ne karo na farko da ake yin taho-mu-gama tsakanin ‘yan sanda da sojoji a Najeriya, lamarin da kan haifar da asarar rayuka.

#BBCHAUSA

Leave a Reply

%d bloggers like this: