Jami’an yan sanda a Abuja sun kama mutane 307 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban.

 

An kama mutanen a Gidan Dambe, Dei-Dei, Zuba, da Abuja.

 

Mai magana da yawun ƴan sanda a Abuja Josephine Adeh ce ta bayyana a wata sanarwa da ta rabawa manema labarai.

 

Daga cikin mutane 307 da aka kama akwai wasu 170 da aka samu da laifi.

 

Sannan akwai wasu mutane biyar da ake zargi da aikata fashi da makami, da kuma muggan kwayoyi.

 

Kamen da aka yi, kwamishinan ƴan sanda ne da kansa ya jagoranta.

 

Kuma sauran da aka kama ba tare da laifi ba bayan an yi bincike, an sadasu da iyalansu.

 

Waɗanda aka samu da laifi kuwa an gurfanar da su a gaban kotu don girbar abinda su ka shuka.

 

Kwamishinan ya ce irin wannan kamen za su ci gaba da yi a kai a kai don ganin an magance matsalar tsaro da aikata laifuka a Abuja.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: