Gwamnatin Jihar Kano ta musanta wata jita-jita da ta ke yawo a Jihar cewa an samu bullar cutar kyanda a Jihar.

Ma’aikatar lafiya ta Jihar ce ta musanta hakan ta cikin wata sanarwa da daraktan kula da lafiya da yaki da cututtuka Dr Imam Wada Bello ya fitar.
Sanarwar ta kara da cewa rahotonni na nuni da cewa an samu bullar cutar ta kyanda ne a wasu sassa na Jihar, wanda kuma rahotan ya bayyana cewa hukumomi ne suka tabbatar da bullar cutar.

Dr Imam ya ce Ma’akatar lafiya na iyaka bakin kokarinta tare da shirin gaggawa a dukkan kananan hukumomi 44 na Jihar, akan dukkan wata cuta da ta ke yaduwa a cikin al’umma ta hanyar daukar matakan da suka dace domin dakile bulla ko yaduwar ta a cikin jama’a.

Dr Imam ya musanta butun ne a yau Laraba, ya kuma bukaci mutane da su yi watsi da rahotannin bullar cutar da ake yadawa a Jihar.
