Gwamnan Jihar Kebbi Nasir Idris ya raba sabbin motoci guda 24 ga ‘yan majalisar dokokin Jihar.

Gwamnan ya mika motocin ga ‘yan Majalisar ne a ranar Talata a gidan gwamnatin Jihar.

Gwamnan ya ce an bai’wa ‘yan majalisar motocin ne domin a saukaka musu ayyukan majalisar.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Ahmad Idris ya rabawa manema labarai, ya ce an bayar da motocin domin yabawa da kyakkyawar alakar aiki a tsakanin bangaren zartarwa da na Majalisa.

Sanarwa ta ce gwamnan ya kuma bukaci ‘yan majalisar da su yi aiki tukuru a yayin gudanar da ayyukannasu.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: