Rundunar ‘yan sanda ta gano wasu fursunoni sama da 300 da ke zaman gidan gyaran hali na Kurmawa a Kano, ba tare da wata takarda ta bayanin shari’arsu ba.

 

Rundunar ta gano hakan ne bayan da babban Sufeta na rundunar, Kayode Egbetokun, ya kafa wani ‘kwamitin lauyoyi mashawarta’ don gudanar da irin wannan binciken.

 

Kwamitin ya gano hakan ne a ranar Laraba a ci gaba da ziyarar da ya ke kaiwa gidajen gyaran hali da kuma gidajen ladabtar da kananan yara.

 

Daily Trust ta ruwaito cewa, kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Muhammad Hussaini Gumel ne ke jagorantar kwamitin.

 

Aikin kwamitin shi ne gudanar da bincike don gano laifukan take hakki na mutanen da ke fuskantar shari’ar manya da kanana.

 

Da yake jawabi ga manema labarai bayan ziyarar, Gumel ya ce aikinsu shi ne gano irin wadannan laifuka, rubuta su da kuma mika su ga hukumomin da abin ya shafa domin daukar matakin da ya dace.

 

Da yake gabatar da wasu fursunonin da ke jiran shari’a na tsawon shekaru a Kurmawa, wani jami’in gidan yarin, ya ce mafi yawansu an kai su ne ba tare da shaidar kama su da laifi ba.

 

Ya kara da cewa wasu daga cikin fursunonin sun shafe shekaru a tsare ba tare da takamaiman kotunan da aka gurfanar da su ba, kuma ba su da bayanan shari’a.

 

Wani fursuna mai suna Ibrahim Dala ya ce ana tuhumarsa da laifin kisan kai amma tun bayan da aka tsare shi a shekara ta 2009 ba a sake kai shi kotu ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: