Ministan makamashi, Bayo Adelabu, ya yi barazanar soke lasisin kamfanonin rarraba wutar lantarki biyo bayan rashin samun wutar lantarki a faɗin ƙasar nan.

 

A wani dogon rubutu da ya yi a shafinsa na X ranar Laraba, Adelabu ya koka kan rashin wadatacciyar wutar lantarki a faɗin ƙasar nan.

 

Adelabu ya bayyana cewa, duk da ƙoƙarin da ake yi na inganta lamarin, wutar lantarki na ci gaba da raguwa a fadin ƙasar.

 

Ministan ya danganta matsalar rashin samun wutar lantarki a Najeriya da rashin aikin da wasu kamfanonin rarraba wutar lantarki ke yi da ɓarnata kayayyakin wutar lantarki a Abuja, Benin, Fatakwal da Ibadan.

 

Adelabu ya ce ya kira shugabannin kamfanonin AEDC, IBEDC, da kuma manajan darakta na kamfanin rarraba wutar lantarki na Najeriya (TCN), zuwa wani muhimmin taro domin kawar da matsalar.

 

Ya ƙara da cewa taron na da nufin tattaunawa kan tabarbarewar wutar lantarki a yankunan tare da samar da mafita mai ɗorewa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: