Babbar kotu da ke zamanta a jihar Kano ta ba da umarnin sake gwajin kwakwalwa ga Hafsat ‘Chuchu’ wadda ake zargi da kisan saurayinta.

Kotun ta umarci duba lafiyar kwakwalwarta a asibitin mahaukata karkashin kulawar gidan gyaran hali na Kurmawa.
Idan ba a manta ba asibitin masu tabin kwakwalwa na Dawanau ta mika rahoto kan gwajin da suka yi a zaman shari’ar da aka yi a baya.

Wadda ake zargin, Hafsat ‘Chuhcu’ da ke rayuwa a Unguwa Uku ta na fuskantar tuhuma kan zargin kisan kai.

Mai Shari’a, Zuwaira Yusuf ta umarci likitoci su sake duba Hafsat don ba da rahoto da sakamako da za a yi hukunci a kai.
Har ila yau, kotun ta ki amincewa da ba da belin mijin Hafsat mai suna Dayyabu Abdullahi da kuma Adamu Muhammad da Nasidi Muhammad kan zargin ba da bayanan karya.
Zuwaira Yusuf ta ce laifukan da ake zarginsu masu girma ne don haka babu damar bayar da beli har sai idan akwai wani dalili mai karfi.
Lauyoyin wadanda ake zargin sun bukaci kotun ta ci gaba da sauraran karar kasa da kwanaki 14 karkashin sashe na 390.
