Yayin da hauhawar farashin kayayyaki ke ƙara tsananta, majalisar wakilai a Najeriya ta yi kira da a biya ma’aikatan Najeriya albashi wadatacce.

Jaridar Daily Trust ta ce majalisar ta kuma umarci kwamitocin kwadago da samar da ayyuka, kuɗi da tsare-tsare da su tsara hanyoyin biyan albashin ma’aikatan Najeriya a farashin da ya yi daidai da yanayin tattalin arziƙin da ake ciki.


Wannan matakin ya biyo bayan amincewa da wani ƙudirin da ƴan majalisa 40 suka goyi baya.
Da yake jagorantar muhawara kan ƙudirin, mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar, Aliyu Madaki, ya ce hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar nan ya sa talakawan Najeriya cikin wahala.
Ya yi nuni da cewa biyan buƙatun yau da kullum da suka haɗa da abinci, ruwa, gidaje, ilimi, kiwon lafiya, sufuri, tufafi, da sauransu na neman gagarar ƴan Najeriya.
Duba da yanayin tattalin arziƙin da ƙasar nan ke ciki, majalisar ta yi nuni da cewa babu wani ma’aikaci da zai iya rayuwa a Najeriya da albashi ƙasa da N100,000 a kowane wata.
