Gwamnan Jihar Neja Umar Bago ya amince da karin albashin wucin gadi na naira 20,000 ga dukkan ma’aikatan jihar.



Gwamnan ya amince da karin albashin ne a taron majalisar zartarwa na Jihar a yau Laraba.
Gwamnan ya ce za a fara biyan karin albashin ne nan take ba tare da an dauki dogon lokaci ba.
A zaman Majalisar gwamna Bago ya bayyana cewa duba da watan azumi da ake ciki gwamnatinsa za ta raba kayan abinci mota 120 ga mabukata a Jihar.
Sanna gwamnan ya ce za kuma a raba dafaffen abinci a gurare daban-daban na Jihar.
Bago ya kara da cewa sun yi hakan ne domin ragewa mutane Jhar radadin halin da ake ciki.
