Gwamnan Jihar Nasarawa Abdullahi Sule ya bayar da umarnin gudanar da bincike akan mutuwar wasu dalibai mata guda biyu na Jami’ar Jihar, da suka mutu a wajen rabon tallafin kayan abinci.

Gwamnan ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ya fitar inda ya nuna rashin jin dadinsa dangane da faruwar lamarin.

Gwamnan ya bayar da umarnin ne ga hukumar makarantar da jami’an tsaro, domin gudanar da binciken kan lamarin tare da binciko masu hannu a ciki.

Sule ya kara da cewa za a ci gaba da rabon kayan abincin, tare da sanya matakan tsaro a yayin rabon.

Daga karshe gwamnan ya kuma mika sakon ta’aziyyarsa ga ‘yan uwa da iyalan wadanda suka rasa rayukansu a Jihar.

Idan baku manta ba a jiya mun baku labarin yadda wasu daliban Jami’a mata a Jihar suka rasa rayukan su a wajen rabon kayan tallafin abinci yayin da kuma 23 suka jikkata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: