Gwamnan jihar Kano ya fitar da sunayan kwamishinoni guda hudu labaran Majalisar Kamaluddeen Sani Shawai ya fitar a yau Talata.

 

Shawai ya ce daga cikin wadanda gwamnan zai nada ciki harda dan tsohon gwamnan Jihar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, wato Mustapha Rabi’u Kwankwaso.

 

Sauran su ne Usman Shehu Aliyu, Adamu Aliyu Kibiya da kuma Abduljabbar Garko.

 

A cewar Shawai za a tantance mutanen ne a ranar 2 ga watan Afrilu mai kamawa.

 

Har ila yau sanarwar da Shawai ya fitar ta ambato cewa Kakakin Majalisar Hon Jibril Isma’il Falgore ya ce nadin Kwaminonin na zuwa ne a lokacin da gwamnan Jihar ya mikawa Majalisar bukatar kafa wasu sabbin Ma’aikatu a Jihar.

 

Falgore ya bayyana cewa daga cikin Ma’aikatun da za a kafa sun hada da Ma’aikatar Jin-kai da Yaki da Fatara, Ma’aikatar Albarkatun Kasa, Ma’aikatar Makamashi da kuma Ma’aikatar Harkokin cikin Gida da Ayyuka na Musamman.

 

Hon Falgore ya ce gwamnan ya bukaci a Kafa sabbin Ma’aikatun ne domin hakan zai taka rawar gani wajen inganta harkokin tattalin arziki da samar da shugabanci nagari.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: