Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ayyana ranakun Litinin da Juma’a a matsayin ranar hutu ga ma’aikata.

 

Za a yi hutun Esta a ranakun Juma’a 29 ga watan Maris da kuma Litinin 1 ga watan Afrilu mai kamawa.

 

Ministan harkokin cikin gida Olubunmi Tunji-Ojo ne ya sanar da hutun yau a madadin gwamnatin tarayya.

 

A sanarwar mai ɗauke da sa hannun Dakta Aishetu Gogi-Ndayako sakatariyar din-din-din a hukumar, sanarwar ta hori yan ƙasar da su kasance masu yafiya, nuna soyayya a ranakun hutun.

 

Sannan aka bukaci mabiya addinin kisita da su yi amfani da lokutan wajen kawo cigaba mai ma’ana a Najeriya.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: