Rundunar sojin saman Najeriya sun samu sanarar tarwaatsa sansanin ƴan bindiga a jihar Zamfara.



Nasarar na zuwa ne a ranar Laraba yayin da sojin su ka kai hari ta sama a kan sansanin ƴan bindiga uku wanda ya yi sanadiyyar lalatasu gaba ɗaya.
Mai magana da yawun rundunar Edward Gabkwet ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai yau a Abuja.
Ya ce sansanin da aka lalata mallaki ne ga rikaƙƙen ɗan bindiga Abdullahi Nasanda a Zurmi, Malam Tukur a Gusau, da wani sansani a ƙaramar hukumar Maradun.
Ya ce bayanan sirri da su ka samu ne ya tabbatar musu da sansanin da mutanen Nasanda ke ɓoye a ciki tare da baburansu.
Haka kuma yayin harin sun hallaka ƴan bindiga da dama.
Jirgin sojin ya kai hari sansanin ƴan bindiga a Kanikawa daa k ƙaramar hukumar Maradun kuma a nan ma ya ƙaddamar da hare-haren a kan ƴan bindigan tare da lalata sansanin baki ɗaya.
