Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa a Najeriya EFCC ta ce ta ƙwato Naira biliyan 32.7 da $445,000 da ake zargin wawushe a ma’aikatar jin ƙai da yaƙi da fatara.

 

Hukumar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa a shafin X da kakakinta, Dele Oyewale, ya fitar a ranar Lahadi, 14 ga watan Afirilun 2024.

 

EFCC ta bayyana hakan ne bayan abin da ta kira yadda ake ta yawan maganganu kan binciken da take yi a ma’aikatar jin ƙai da yaƙi da fatara.

 

Oyewale ya yi bayanin cewa a farkon binciken da hukumar ta fara, ta gayyato tsofaffi da dakatattun jami’an ma’aikatar domin jin daga bakinsu.

 

A cewar kakakin na EFCC, hukumar ta kuma fara binciken wasu ayyukan zamba da suka haɗa bashin da aka ciyo daga bankin duniya, kuɗaɗen Covid-19 da kuɗaɗen da aka karɓo na Abacha waɗanda aka ba ma’aikatar domin rage raɗaɗin talauci.

 

A farkon fara bincike, an gayyato tsofaffi da dakatattun jami’an ma’aikatar jinƙai, kuma binciken da ake yi kan zargin zamba ya sanya ya zuwa yanzu an ƙwato N32.7bn da $445,000.

 

Binciken kuma ya bankaɗo jami’an ma’aikatar masu yawa waɗanda ake zargin da hannunsu wajen yin sama da faɗi da kuɗaɗen.

 

Rundunar yan sandan a jihar Osun sun kama wani maidanci bisa laifin kashe mahaifiyarsa.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: