Hukumomin Jami’ar Jihar Filato sun sanar da rufe jami’ar da ke cikin karamar hukumar Bokkos ta Jihar bisa yadda matsalar rashin tsaro ke kara ta’azzara a yankin.

Magatakardar jami’ar Yakubu Ayuba ne bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.

Hukumomin makaranta sun bayyana cewa sun rufe makaran ne sakamakn wani hari da ‘yan bindiga su ka kai kauyen Chikam da ke kusa da jami’ar inda su ka hallaka wasu dalibai biyu a jami’ar.

Hukumar Jami’ar ta bayyana cewa sun bayar da hutun ne na tsawon kwanaki goma wanda hakan zai ba daliban kariya daga yawaitar hare-haren ‘yan bindiga tare kuma da neman hanyar inganta tsaro kafin dawowarsu karatu.

Magatakardar ya kara da cewa jami’ar ta kuma dakatar da dukkan wata jarabawar karshen zangon karatu na farko da dalibai ke zanawa a halin yanzu har zuwa ranar 2 ga watan Mayu mai kamawa.

Bayan kai harin gwamnan Jihar Caleb Mutfwang ya nuna bacin ransa bisa harin da aka kai jam’iar da kauyukan da ke kusa da ita.

Gwamnan ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da daraktan yada labaran gwamnan Gyang Bere ya fitar a ranar Juma’a, inda gwamnan ya yi kira da a kara inganta tsaro a Jihar domin kare rayukan al’ummar yankunan Jihar.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: