Shugaban Kasa Bola Tinubu ya yi alkawarin cewa Najeriya za ta dogara da kanta wajen samar da wadataccen abinci a cikin Mulkinsa.

Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a yayin da yake kaddamar da fara aikin titin Bidda zuwa Minna a Jihar Neja.

Shugaban wanda ya samu wakilcin ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa Muhammad Idris ne ya ba da tabbacin hakan.

Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta yi aiki kafada-da-kafada da Jihohi domin samar da wataccen abinci a Kasar.

Shugaban ya kara da cewa gwamnatin tarayya za ta tallafawa Jihar Neja da sauran jihohin Kasar domin samar da ci gaba mai dorewa a fadin Kasar.

Shugaban ya kuma ce za su gina tituna masu nagarta domin kare rayuka da kuma bude hanyoyin bunkasar tattali arzikin kasar.

Sannan shugaban ya kuma bukaci da sauran gwamnonin Jihohi da su yi koyi da irin namijin kokari da gwamnan na Neja Umar Muhammad Bago a Jiharsa.

Aikin ginin titin zai lashe Naira biliyan 169.7 a gurin gininsa.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: