Wasu yan bindiga sun rufe babbar hanyar Gusau zuwa Funtua tare da yin garkuwa da mutane da dama.

An yi garkuwa da matafiya wadanda ba aa kai ga gano adadin yawansu ba.
Yan bindigan sun tare baabbar hanyar da ke tsakanin Jucheri da Magazu a ƙaramar hukumar Tsafe yayin da su ka fara harbe harbe.

Mai magana da yawun yan sanda a jihar Yazid Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin

Ya ce ba a gano adadin yawan mutanen da aka sace ba.
Amma su na aiki tare da sauran jami’an tsaro don ganin an kubutar da mutanen da aka sace.
Lamarin ya faru ne a yammacin jiya Asabar.
Sannan ya musanta zargin sace yan sandan kwantar da tarzoma biyar da ake yadawa an yi.