Ministan sadarwa a Najeriya Dakta Bosun Tijani ya ce za a ƙara kuɗin kiran waya a ƙasar amma ba da kaso 100% ba.

 

A cewar ministan, su na kan tattaunawa kan batun yayin da su ka fara wani zama da masu ruwa da tsaki a ɓangaren jiya Laraba.

 

Ministan ya tabbatar da cewar za a kara kudin kira daga kamfanonin sadarwa na kasar wanda su ka buƙaci yin haka tun tuni.

 

A wani zama da ministan ya jagoranta jiya Laraba, ya ce an gayyaci masu kamfaonin sadarwa a ƙasar da kuma shugabanin hukumar sadarwa domin tattaunawa a kan batun.

 

A cewarsa, hukumar sadarwa ta NCC za ta fitar da umarnin da za ta bayar na ƙarin amma ba zai zama kaso ɗari ba kamar yadda kamfanonin su ka buƙata.

 

Tun a baya ne kamfanonin ke bayyana cewar ba za su iya ci gaba da gudanar da ayyukansu ba matuƙar ba su ƙara kuɗin kira da aika sako da kuma data a Najeriya ba.

 

Sai dai ministan ya ce ba zai bar gwamnati ta ci gaba da barin kamfanonin na yin yadda suke so a bangaren ba, wajibi ne ta shiga ciki domin ba za ta barsu su kaɗai ba.

 

Kamfanonin sun ce matukar ana son samun ingantattun hanyoyin sadarwa a ƙasar to ya zama wajibi su ƙara kuɗin kira da sauran hanyoyin shigar kudade na kamfanonin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: