Rundunar ‘yan sandan Jihar Sokoto ta tabbatar da yin garkuwa da wasu masallata da ke sallah a wani masallaci da ke Unguwar Bushe a Karamar hukumar Sabon Birni a Jihar.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar DSP Ahmad Rufa’i ne ya tabbatar da hakan a yau Juma’a.
Maharan sun sace mutanen ne a lokacin da su gudanar da Sallar Asubahin jiya Alhamis, inda suka yi garkuwa da mutane kimanin Goma ciki harda Limamin Masallacin.

Ahmad Rufa’i ya bayyana cewa sun samu labarin faruwar lamarin ne daga Baturen ‘yan sandan Unguwar ta waya.

Kakakin ya ce bayan garkuwa da mutanen, tuni jami’ansu hadin gwiwa da sauran jami’an tsaro ke gudanar da bincike don ganin sun kubtar da mutanen da aka sace.
