Gwamnan jihar Ondo Lucky Ayidatiwa ya yi wa masu laifi 43 afuwa.

Gwamnan ya bayyana haka ne cikin jawabinsa bayan rantsar da shi a matsayin sabon gwamnan jihar.
A cikin jawabinsa, gwamnan ya ce yi wa mutanen afuwar ne karkashin dama da ikon da yake da shi a matsayinsa na gwamna.

Gwamnan ya sha rantsuwar kama aikin ne a filin wasa na jihar da ke Akure bayan lashe zaɓen gwamnan watanni biyu da su ka gaba.

A cewarsa, shi da mataimakinsa ba za su sarara ba har sai sun tabbatar sun aiwatarwa da al’ummar jihar abinda su ka alƙawarta musu.
A cewarsa, gwamnatinsa za ta mayar da hankali wajen janyo hankalin masu zuba hannun jari a jihar don farfaɗo da harkoki.
Rantsuwar ta samu halartar jigajigan jam’iyyar APC ciki har da shugabanta na ƙasa Abdullahi Ganduje da gwamnonin Legas, Ogun da Osun da ministan harkokin cikin gida Tunji Ojo.
