Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa ta kara karfafa ayyukan hukumomin tsaron Kasar don kara shawo kan matsalar rashin tsaro da ake fuskantar kasar.

Shugaban ya bayyana hakan ne a gurin taron koli na manyan jami’an ‘yan sanda karo na biyar a garin Abeokuta da ke jihar Ogun.

Shugaban wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Sanata Kashim Shettima , ya bayyana cewa gwamnatinsa na samar da kayan aiki ga jami’an tsaro da nufin kawo karshen matsalar rashin tsaro da kuma yaki da aikata laifuka a fadin Kasar.

Shugaba Tinubu ya kuma bayyana kudurin gwamnatinsa na kara karfafa ayyukan jami’an ‘yan sanda ta hanyar samar musu da kyakkyawan yanayi da kayan aiki.

A karshe shugaban ya yi kira ga al’ummar Kasar da su hada kai da jami’an tsaron ‘yan sanda domin tabbatar da tsaro a Kasar, inda ya ce nasarar ba za ta samu ba sai da goyan bayan al’umma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: