Jam’iyyar APC ta kasa ta nuna takaicinta bisa kalaman da tsohon gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Elrufa’i yayi akan shugaban Kasa Bola Tinubu da mai bai’wa shugaban shawara kan sha’anin tsaro Malam Nuhu Ribadu.

Mataimakin shugaban Jam’iyyar na Kasa a yankin Kudu maso gabashin Kasar nan, Dr Ijeoma Arodiogbu ne ya bayyana hakan a lokacin da yake mayar da martani ga Elrufa’i.

A hirar da aka yi da El-Rufai a jiya Litinin, ya nuna takaicinsa akan sauye-sauyen tattalin arziƙin da ake samu a gwamnatin shugaba Tinubu, inda ya bayyana hakan a matsayin wanda bai kamata ba.

Sannan a cikin kalaman na El-Rufai ya soki naɗin da shugaba Tinubu ya yi wa Ribadu, inda ya ce ko kadan Ribadu bai dace da mukamin ba.

Har ila yau kuma Elrufai ya zargi Ribadu da gwamnan Jiharsa ta Kaduna Uba Sani da shirin dakile nasararsa a zaben shekarar 2031 mai zuwa.

Amma a martanin Jam’iyyar ta APC ya bayyana Elrufa’i a matsayin mutum mai son zuciya, da bai samu cikar burinsa ba na gaza yin son kai a cikin gwamnatin shugaba Tinubu.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: