Shugaban Kasa Bola Tinubu ya rattaba hannu akan kasafin kudin shekarar 2025 wanda ya kai naira tiriliyan 54.99.

A ranar 13 ga watan Fabrairun nan ne majalisar dokokin Kasar ta amince da kasafin na Naira Tiriliyan 49.7 da shugaban ya gabatar mata, bayan kammala yin nazari akan shi, da kuma yin kari.
Shugaban ya sanya hannu akan kasafin ne a yau Juma’a a fadarsa da ke birnin tarayya Abuja.

Kasafin kudin shekarar nan ta 2025 ya wuce na shekarar 2024 da ta gabata wanda ya kai naira tiriliyan 27.5 da kashi 99.96 cikin 100.

A cikin kasafin an tsara kashe naira tiriliyan 14.32 wajen biyan bashi, yayin da kuma manyan ayyuka za su lashe naira tiriliyan 23.96, da dai sauran.