Kungiyar kwadago a Najeriya NLC ta janye daga shirin tafiya yajin aikin da ta kudiri aniyar yi a farkon watan Maris.

Hakan ya biyo bayan wani zama da aka yi tare da cimma matsaya.

Kungiyar ta dauki aniyar tafiya yakin aikin a ranar 1 gawatan Maris sakamakon karin kuɗin kira, data da aika sakonni da gwamnatin tarayya ta amincewa kamfanonin sadarwa su yi.

Sai dai a wani zama da kungiyar ta yi da tsagen gwamnatin, sun cimma matsaya za a mayar da karin ya koma kaso 35.

Sannan an kafa wani kwamitin mutane goma da zai tabbatar an aiwatar da yarjejeniyar.

Kamfanin sadarwa a Najeriya sun ce ba za su iya ci gaba da ayyukansu ba har sai sun y karim da kaso 100.

Batun da gwamnatin ta ki aminta da shi sai dai ta sahale musu su yi karin da kaso 50.

Leave a Reply

%d bloggers like this: