Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya Sanata Natasha Akpoti-Uduagha ta yi kira ga matar Shugaban Majalisar Dattawa Ekaette Akpabio da ka da ta shiga rikicin da ke faruwa tsakaninta da mijinta.

Sanata Natasha ta bukaci da matar ta Akpabio da ta kauracewa shiga rikicin da ke faruwa tsakaninta da Akpabio.
A wata takarda da Natasha ta aikewa da matar Akpabio ta hannun lauyanta Victor Giwa, ta gargade ta da ta gujewa sanya baki a cikin lamarin.

Har ila yau Sanata Natasha ta tabbatar da cewa tana da kwararan hujjojin da za ta bayyana akan zargin da take yi masa, inda ta bukaci da Ekaette da ta bar Akpabio ya fito ya kare kan shi akan zargin da ta ke yi masa.

