Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya miƙa taaziyya ga iyalan attajiri a Kani Alhaji Nasiru Ahali.

A wata sanarwa da daraktan yaɗa labaransa Sanusi Nature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu, gwamnan ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashin jigo.

Ya ce Alhaji Ahali guda ne cikin mutanen da su ka kafa masana’antu waɗanda su ka taimaka wajen bunkasar tattalin arzikin jihar

Gwamnan da muƙarrabansa da ma al’ummar jihar sun miƙa taaziyya babban rashin.

Ya ce ba rashi ne ga iyalansa kadai ba, rashi ne ga al’ummar Kano da ma ƙasa baki daya

Alhaji Nasiru Ahali ya rasu jiya Alhamis da daddare ya na da shekara 108 a duniya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: