Gwamnan riko na Jihar Rivers Ibok-Ete ya nada Farfesa Ibibia Lucky Worika a matsayin sabon Sakataren gwamnatin Jihar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar daga fadar gwamnatin Jihar a yau Talata.
Sanarwar ta bayyana cewa nadin Lucku ya biyo bayan yin nazari kan ƙwarewa da gogewarsa a bangarori daban-daban.

Sanarwar ta kuma ce nadin Worika ya kuma yi daidai da manufarsa ta amfani da kwararru daga jihar Rivers domin samar da tabbataccen zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar.

Nadin Sakataren na kuma zuwa ne a daidai lokacin da gwamnan rikon ya amince da yin murabus din Shugaban Ma’aikatan gwamnatin Jihar George Nwaeke.
Inda kuma gwamnan rikon ya nada Iyingi Brown wanda ya kasance babbar sakataren ofishin shugaban Ma’aikatan Jihar, inda kuma zai zauna a matsayin mai rikon mukamin shugaban Ma’aikatan har zuwa lokacin da za a nada wani sabon shugaban Ma’aikatan.