Labarai
Hukumomin Tsaro A Kano Sun Dakatar Da Hawan Sallah

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaron Jihar, sun dauki matakin dakatar da hawan sallah da aka saba yi duk shekara a Jihar.

A wani taron manema labarai da aka gudanar a hedkwatar ‘yan sanda ta Kano da ke Bampai a yau Juma’a, Kwamishinan ‘yan sandan rundunar Ibrahim Adamu Bakori ya ce an hana hawan ne don tabbatar da zaman lafiya a Jihar.
Bakori ya ce sun dauki matakin ne bisa samun rahotonnin tsaro da kuma tattaunawa da gwamnatin Kano da masu ruwa da tsaki a bangaren tsaro, domin tabbatar da zaman lafiyar al’ummar jihar.

Bakori ya kara da cewa rundunar za ta aike da jami’anta a sassan jihar domin tabbatar da ganin an bi doka da oda kafin sallah da kuma lokacin bukukuwan sallar.

Kwamishinan ya kuma bukaci al’ummar jihar da su gudanar da sallar cikin kwanciyar hankali, ba tare da tashin hankali ba.
Bakori ya ce an kuma hana hawan doki don yin kilisa, ko tsren motoci, ko kuma tukin gangaci, da dai sauran ayyukan da suka sabawa doka.
Sannan rundinar ta bukaci al’umma da su kai rahoton dukkan wani abu da ba su gamsu da shi ba ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa da su.
Labarai
Atiku Ya Yi Alhinin Rasuwar Dutsen-Tanshi

Tsohon mataimakin shugaban Kasa Alhaji Atiku Abubakar ya mika sakon ta’aziyyar ga ‘yan uwa da iyalan fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya Sheikh Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi bisa rasuwarsa.

Atiku ya mika sakon ta’aziyyar ne ta cikin wata wallafa da ya fitar a yau Juma’a.
Atiku ya bayyana Duten-Tanshi a matsayin mutum nagartaccen mutum da ya sadaukar da rayuwarsa wajen yada ilimi da neman zaman lafiya a tsakanin al’umma.

Tsohon Mataimakin shugaban Kasar ya bayyana Dutsen Tanshi a matsayin malamin da koyarwarsa ta taimaka wajen gyara tarbiyya da ɗabi’un al’umma.

Atiku ya kara da cewa rashin Malamin babba rashi ne ga dukkan al’ummar Musulmi na Jihar Bauchi,dama kasa baki daya, bisa yadda Malamin ke amfanar da al’umma.
Alhaji Atiku ya yi addu’ar neman gafara da rahma ga Mallamin, tare da sauran Al’ummar musulmi.
Labarai
Kotu Ta Hana Natasha Da Akpabio Hira Da Manema Labarai

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da shugaban majalisar dattijai Sanata Godswill Akpabio daga yin hira da ‘yan Jaridu ko yin wallafa akan shari’ar da ke gaban kotu.

A hukuncin da Kotun ta yanke a yau Juma’a karkashin mai shari’a Binta Nyako, ta ce daga yanzu babu wani bangaren da zai sake hira da ‘yan jaridu akan sabanin da ke tsakanin bangarorin.
Nyako wadda ta amshi shari’ar daga hannun Mai shari’a Obiora Egwuatu ta ce hakan na da matukar muhimmanci domin tabbatar da ganin an yiwa kowa adalci.

Mai shari’a Nyako ta haramtawa Natasha da Akpabio da kuma lauyoyinsu yaɗa zaman shari’ar kai-tsaye a shafukan sada zumunta.

Kotun ta yanke hukuncin bayan karar da lauyan da ke kare Akpabio ya shigar yana mai cewa Sanata Natasha na zuwa gidajen talabijin daban-daban domin yin hira da ita akan shari’ar duk da cewa lamarin na a gaban kotu.
Labarai
Hakeem Baba-Ahmad Ya Yi Murabus Daga Matsayin Mai Bai’wa Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Siyasa

Mai bai’wa shugaban Kasa shawara kan harkokin siyasa Hakeem Baba Ahmad ya yi murabus daga kan mukaminsa.

Wata majiya daga fadar shugaban Kasa a jiya Laraba, ta ce tsohon mai magana da yawun kungiyar dattawan Arewa NEF ya mika takardar murabus dinnasa kimanin makonni biyu da suka gabata.
Babu cikakken bayani kan murabus dinnsa, sai dai Hakeem ya ce yayi murabus din ne bisa dalilai na ƙashin kai.

Sai dai har yanzu ba a tabbatar da ko fadar shugaban ƙasa ta amince da murabus dinnasa ba.

Shugaba Tinubh ya nada Hakeem Baba-Ahmed ne a matsayin mai bai’wa mataimakin shugaban Kasa Kashim Shettima shawara kan harkokin siyasa a watan Satumba 2023.
A watanni 17 da Hakeem ya kwashe yana aiki, ya wakilci fadar shugaban kasa a gurare da dama, ciki har da wani babban taron kasa kan inganta dimokuradiyya wanda aka gudanar a ranakun 28 da 29 ga watan Janairu 2025 a Abuja birnin tarayya Abuja.
A wasu lokutan Dr. Hakeem ya na shan suka a fadar shugaban ƙasa musamman daga Ƙaramin Ministan Tsaro Mohammed Bello Matawalle.
Yayin da a watan Afrilu 2024 Matawalle ya soki Hakeem Baba-Ahmed bayan kare kungiyar NEF, bayan ministan ya bayyana kungiyar a matsayin wadda ba ta da tasiri a siyasa.
Wannan dai na zuwa ne bayan da ƙungiyar NEF ta ce yankin Arewa ya yi kuskure da zaben Shugaba Tinubu a 2023.
Hakeem Baba-Ahmed ya ce zai fi dacewa ministan ya bayyana irin gudunmawar da ministocin Arewa suka bayar a gwamnatin Tinubu maimakon sukar kungiyar.
-
Labarai1 year ago
Mafi Karancin Sadaki A Najeriya Ya Koma Dubu 99,241
-
Mu shaƙata2 years ago
Kun San Ma’anar Kalmar Chiza Dani? Waƙar Da Ke Tashe A Kwanakin Nan?
-
Labaran ƙetare6 years ago
Wajibi ne duk wani namiji ya Auri mata Biyar ko a ɗaure shi a gidan yari— Sarkin Swaziland
-
Al'ada6 years ago
Fahimta ta a kan matsalar aure a ƙasar Hausa
-
Labarai6 years ago
Ba kwaya ƴan sandan kano suka kama ba, babu sinadarin maye a cikin maganin – NAFDAC
-
Addini5 years ago
Lokutan da ake saurin karɓar addu’a
-
Lafiya6 years ago
Menene Genotype ? Amfanin yinsa kafin Aure – Mujallar Matashiya
-
Mata adon gari6 years ago
Sinadarin gyaran gashi – Adon Gari