
Daga Abdulrasheed Rabiu Rigasa
Hukumar ’yan sanda ta Najeriya ta sanar da cewa ta tura jami’anta wurare masu muhimmanci a faɗin ƙasar domin shirin zanga-zangar da kungiyoyin Take-It-Back Movement da wasu ƙungiyoyin fararen hula suka tsara gudanarwa a yau Litinin, don nuna ƙin amincewa da tsadar rayuwa, take haƙƙin ɗan Adam, da rikicin siyasa a jihar Rivers da ma sauran wasu jahohin kasar.

Hukumar ta shawarci masu zanga-zangar da su dakatar da shirinsu, tana mai cewa hakan bai dace da wannan lokaci ba, kamar yanda ta wallafa a shafin ta na facebook a yammacin jiya Lahadi.

Rundunar ta baiyana cewa “Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta samu rahoton cewa wani gungu da ke kira kansu “Take It Back Movement” na shirin gudanar da zanga-zanga a jihohi daban-daban na Najeriya, musamman a Babban Birnin Tarayya, Abuja, a ranar Litinin 7 ga Afrilu, 2025. ranar da Gwamnatin Tarayya ta ware a matsayin Ranar ‘Yan Sanda ta Kasa, domin murnar jajircewa da sadaukarwar jami’an ‘yan sanda wajen tabbatar da tsaron kasa.
Duk da cewa Rundunar ‘Yan Sanda ba ta da matsala da ‘yancin yin taro da bayyana ra’ayi cikin lumana kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya tanada, ta nuna damuwa matuka kan dalilan da ke goyon bayan zaben wannan rana domin gudanar da zanga-zanga, wadda ta zo daidai da ranar bikin girmama gudummawar da Rundunar ke bayarwa wajen kare Najeriya. Wannan biki mai armashi zai tattaro manyan baƙji daga ciki da wajen kasa, ciki har da tsofaffin Sufeto Janar na kasashen waje da jakadu.”
Ta cigaba da cewa “A bisa tsarin da ake bi a duniya wajen karrama hukumar ‘yan sanda, Gwamnatin Najeriya ta dauki matakin ayyana kowace ranar 7 ga Afrilu a matsayin Ranar ‘Yan Sanda ta Kasa. Amma aiwatar da zanga-zanga a wannan rana na iya zama wata manufa ta boye wacce ake kallonta a matsayin aikin rashin kishin kasa da kuma wanda ka iya bata sunan Rundunar ‘Yan Sanda da Najeriya baki ɗaya” inji hukumar
Rundunar ‘Yan Sanda ta kuma shawarci masu shirin gudanar da wannan zanga-zanga da su dakatar da ita, domin ba a yanzu ya kamata a gudanar da wannan zanga-zanga ba, sannan rundunar ta kuma yi kira ga masu shirya wannan zanga-zanga da sauran mutane da ke shirin halarta da su nemi mafita ta hanyar tattaunawa da hukumomin gwamnati da suka dace don gabatar da bukatunsu cikin lumana.
A daya bangaren kuwa Shugaban ƙungiyar Take-It-Back Movement, na ƙasa Juwon Sanyaolu, ya ce za su ci gaba da zanga-zangar duk da barazanar jami’an tsaro. Ya ce zanga-zangar na da nufin kalubalantar amfani da dokar Cybercrime da kuma nuna damuwa kan tsarin mulki da ya tabarbare.
Ya ce: “Ba za mu fasa zanga-zangar ba. Muna da haƙƙin yin hakan. Abin da ya faru lokacin zanga-zangar #EndBadGovernance abin kunya ne ga demokradiyya. An kashe mutane, yara ƙanana aka kama. Shugaban kasa da IGP yakamata su sake tun tuni.” inji shi.
Mu dai anan sai muce Allah ya kawo mana zaman lafiya da cigaba mai ɗorewa a kasar mu Najeriya da ma duniya baki daya.