Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi gargaɗin cewa jami’an gwamnati da ba su da ilimi kan kafofin watsa labarai suna cikin haɗarin faɗawa tarkon yarda da labaran ƙarya.

 

Mataimaki na musamman ga Ministan kan yaɗa labarai, Rabiu Ibrahim, ya faɗa a takardar sanarwa ga manema labarai cewa Idris ya yi wannan bayanin ne a ranar Talata a birnin Abuja, a wajen Taron Masu Magana da Yawu karo na biyu wanda Cibiyar Ƙwararrun Masana Hulɗa da Jama’a ta Nijeriya (NIPR) ta shirya tare da haɗin gwiwar Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai.

 

Ya ce: “Ina so in yi amfani da wannan dama ta wannan taron na ƙwararru domin jaddada muhimmancin rungumar abin da ake kira ‘Information and Media Literacy’, wata haɗaɗɗiyar ƙwarewa da Ƙungiyar Ilimi, Kimiyya, da Al’adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNESCO) ta fara gabatarwa a shekarar 2008, wadda ke haɗa dabarun fahimtar bayanai da fahimtar kafofin watsa labarai.”

 

A cewar Ministan, samun wannan ƙwarewar ya zama wajibi a wannan zamani da kowa da kowa – wato daga masana hulɗa da jama’a zuwa shugabannin kamfanoni – yake taka rawa a matsayin mai magana da yawun wani.

 

Idris ya ce: “Yau a wannan zamani da kowa ke zama mai magana da yawu – ko ɗan hulɗa da jama’a ne ko shugaban kamfani a ɓangaren gwamnati da masu zaman kan su – wajabcin samun ilimi kan kafofin watsa labarai ya zama abu mai matuƙar muhimmanci, domin yana ba da damar fahimta, nazari da tantance sahihancin saƙonnin da ke yawo a kafafen watsa labarai, wanda hakan zai ba da damar yanke sahihin hukunci da mu’amala da labarai yadda ya kamata.

 

“A ‘yan kwanakin nan, saboda rashin wannan ilimi – wato rashin iya nazarin abin da ke cikin kafafen labarai da tantance sahihancin sa – jami’an gwamnati da ma al’umma gaba ɗaya sun fara faɗawa tarkon labaran ƙarya da yaɗa bayanan da ba su da tushe.”

 

Ya ce samun wannan ilimi zai ba da dama ga masu magana da yawun hukumomi su inganta dabarun su wajen tantance sahihancin labarai, gano son zuciya ko ɓangaranci a cikin su, da kuma amfani da hanyoyin bincike da tantance gaskiya.

 

Domin cimma wannan buri, Ministan ya bayyana cewa ma’aikatar sa ta kusa kammala shiri domin buɗe Cibiyar Ilimin Kafofin Watsa Labarai ta UNESCO – wacce za ta kasance ta farko a duniya – a Buɗaɗɗiyar Jami’ar Ƙasa ta Nijeriya (NOUN) da ke Abuja.

 

Ya ce: “Na dawo daga Paris, a ƙasar Faransa, kwanan nan inda na gana da manyan jami’an UNESCO, kuma buɗe wannan cibiyar ya kasance babban maudu’i a tattaunawar.”

 

Ministan ya kuma bayyana cewa ma’aikatar sa ta samu gagarumar nasara a bara, inda aka samar da sabon matsayi na “public relations” a cikin tsarin aikin Gwamnatin Tarayya.

 

“Abin da wannan ke nufi shi ne, ‘Public Relations’ yanzu yana da nasa hanyar aikin kai-tsaye a cikin aikin gwamnati tun daga watan Disamba 2023.

 

“Haka nan, tsohuwar muƙamin ‘Information Officer’ yanzu an sake masa suna zuwa ‘Information and Public Relations Officer’, da kuma ‘Executive Officer (Information and Public Relations)’.

 

“Ina kuma so in ƙara da cewa NIPR ce ta taka rawar gani wajen ganin wannan cigaba ya samu.”

 

Idris ya kuma jaddada cewa gwamnatin Tinubu za ta ci gaba da goyon bayan ‘yancin faɗar albarkacin baki da kuma ƙarfafa kafafen watsa labarai masu zaman kansu.

 

Ya ce: “A ɓangaren mu, za mu ci gaba da faɗaɗa hanyoyin sadarwa a ƙasar nan da kuma bunƙasa damar zuba jari da tattalin arziki da ke cikin ta.”

 

Har ila yau, Ministan ya yaba wa shugaban NIPR, Dakta Ike Neliaku, saboda ƙara sabon ɓangare mai muhimmanci a wannan taro, wato ‘Information Ministerial Clinic’, inda tsofaffin ministocin yaɗa labarai suka raba gogewar da suka samu da abubuwan da suka fuskanta yayin gudanar da aikin su.

 

Tsofaffin ministocin da suka halarci buɗaɗɗen taron sun haɗa da Farfesa Jerry Gana, Cif John Nwodo, Mista Frank Nweke (Jnr), Mista Labaran Maku, da Alhaji Lai Mohammed.

Leave a Reply

%d bloggers like this: