Wasau da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai’wa jami’an tsaron NSCDC hari a ƙauyen Igbomotoru da ke cikin ƙaramar hukumar Southern Ijaw a Jihar Bayelsa.

Maharan sun kai’wa jami’an tsaron na NSCDC hari ne a ranar Juma’a, inda suka hallaka daya daga cikinsu a lokacin da suke tsaka da gudanar da sintiri a yankin.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa wani Mazaunin yankin ya tabbatar da mata da faruwar lamarin.

Mazaunin yankin ya ce lamarin ya faru da jami’an ne a lokacin da suke gudanar da sintirin, kuma na kan hanyarsu ne ta dawowa daga wani sumame da suka gudanar a guraren da ake haƙar mai ba bisa ƙa’ida ba.

Majiyoyi sun bayyana lamarin a matsayin wani shiri da wasu ƴan bindiga suka yi, inda suka buɗe wuta akan jirgin ruwa jami’an na NSCDC ke gudanar da sintiri akan shi a kusa da Koluama, gurin da ya kasance cibiyar satar mai ce.
Sai dai ana zargin cewa harin baya rasa nasaba da masu lalata bututun mai, da ake zargin sun yi amfani da makamai wajen dakile yunkurin jami’an tsaron.
Rahotanni sun bayyana cewa jami’an da ya rasa ransa an harbe shi ne a yayin musayar wuta, inda kuma sauran jami’an da suka jikkata ke karbar magani a wani babban Asbiti da ke Garin Yenagoa babban birnin Jihar.
Kakakin hukumar ta NSCDC na Jihar Solomon Ogbere a yau Lahadi, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce amma ba shi da cikakken bayanin faruwar lamarin.
Sai dai Kakakin ya ce a gobe Litinin zai fitar da cikakken bayanin faruwar lamarin bayan kammala tattara bayanai