Gwamnan Jihar Jigawa Malam Umar Namadi ya bukaci ƴan Najeriya da su yi watsi da Kalaman Theophilus Danjuma tsohon Ministan Tsaro, na cewa ƴan Najeriya su tashi su kare kansu daga hare-haren ƴan ta’adda a Ƙasar nan.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin wata hira da Channels TV, Namadi ya ce ko kadan Najeriya ba ta kai wannan matakin ba, na daukar matakin kare kansu ba.
Acewar gwamnan irin waɗannan kalaman ka iya haifar da rudani, da rikici da kuma tabarbarewar doka.

Tsohon Ministan tsaro a Najeriya Danjuma ya bukaci yan Najeriya da su tashi domin kare kansu, bisa ƙaruwar ta’azzarar matsalar rashin tsaro a wasu daga cikin sassan Kasar.

Sai gwamna Umar Namadi ya bayyana cewa kalaman ka iya dakula al’amura, yana mai cewa a halin yanzu akwai hanyoyi masu tarin yawa da gwamnati ke amfani da su wajen ganin ta kawo karshen matsalar rashin tsaron Kasar nan.