Tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Elrufai ya ce ya fice daga jam’iyya APC ne domin kawo ƙarshen siyasar ubangida.

Elrufai wanda ya koma jam’iyyar SDP ya bayyana haka ne yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai yau a Kano.
A cewarsa, masu yin siyasar ubangida su ne su ka rusa jam’iyyar APC da ya bari.

A wata ziyasa da Elrufai ya kai wa sarki Muhammadu Sanusi ll, tare da ganawa da jagororin jam’iyyar domin gina kyakkyawan tubali daga tushe
Ya ce jihar Kano ita ce babbar jiha da ke da wahalar sha’ani a siyasa, sai dai su na kan duba hanyoyin da za su samar da nasara.

A cewarsa, su na tsammanin shigar mutane miliyan uku cikin jam’iyyarsu ta SDP.
Ya ce zahirin siyasar Najeriya ya sauya.
Kalaman na Elrufai dai na nuni da zargin an yi masa butulci a jam’iyyar APC wanda a baya har ya ce Allah ba zai bar waɗanda su ka yi masa butulci ba.