Gwamnan Jihar Jigawa Malam Umar Namadi ya karbi wasu ƴan Jam’iyyar PDP da NNPP da suka sauya sheka zuwa Jam’iyyar APC a Jihar.

Gwamnan ya karbi masu sauya shekar ne a jiya Lahadi, tare da yin maraba ga masu sauya shekar zuwa cikin Jam’iyyar ta APC.

Masu sauya shekar sun koma APC a yayin wani taro da ake gudanarwa tsakanin gwamnatin Jihar da Al’ummar gari, inda taron ya kasance karo na shida kuma an gudanar da shi ne a garin Buji da ke Jihar.

Gwamna Malam Umar Namadi ya tabbatar da cewa jam’iyyar APC na maraba da su, inda ya ce za su tabbatar da ganin an bai’wa kowa dama a cikin Jam’iyyar.

Aƙarshe gwamnan ya yi kira ga masu sauya shekar da su ci gaba da bayar da shawarwari masu amfani, don ganin manufofi da kudurin jam’iyyar ta APC ya amfanar da al’ummar Jihar.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: