Wasu da ake kyauta zaton yan bindiga ne sun yi garkuwa da wata Harira Abdullahi matar dagacin Aboro da ke ƙaramar hukumar Sanga a jihar Kaduna.

An yi garkuwa da matar da kuma ƴarsu a jiya Lahadi.
Yan bindigan sun shiga garin da ƙarfe 07:36pm na yammacin jiya Lahadi sannan su ka tafi da su.

Wasu mazauna garin da su ke tabbatar da haka, sun ce harin ya jefa al’ummar yankin cikin fargaba.

Sai dai sun yi wani gangami domin kuɓutar da mutanen da aka sace.
A ƙoƙarin da su ka yi na kuɓutar da su yan bindigan sun buɗe wuta tare da hallaka wani Umar Abdullahi da kuma wani Suleiman wanda aka yi wa rauni yayin da yake asibiti ana kula da shi.
Sai dai yan sanda ba su ce komai a kai ba.