Wata kotun soji da ke zamanta a runduna ta 82 a Jihar Enugu ta yankewa wani jami’in soja mai suna Adamu Muhammad hukuncin kisa ta hanyar rataya, bisa hallaka wata budurwarsa mai suna Hauwa Ali.

A yayin da yake tabbatar da hukuncin Shugaban kotun, Birgediya Sadisu Buhari, ya bayyana cewa Kotun Sojin ta yankewa Adamu hukuncin kisan ne ta kan zarginsa da aikata kisan kai.
Mukaddashin mai magana da yawun rundunar Laftanal Kanal Jonah Unuakalu ya shaudawa manema labarai a yau Talata a birnin tarayya Abuja.

Ya ce bayan yin zurzurfan nazari da kwamitin kotun ya yi, tare da sauraron shaidu aka yankewa sojan hukuncin.

Ya kara da cewa laifin na a karkashin sashe na 106 (a) na dokar sojojin Najeriya, Cap A20 LFN 2004, kuma hukuncin ya yi daidai da abin da doka ta tanada.
A ganawar ta sa da manema labarai Jonah ya kuma ce kotun ta kuma sake yankewa wani Soja mai suna Private Abubakar Yusuf hukuncin ɗaurin shekaru Goma a igidan ajiya da gyaran hali, bisa kamashi da laifin fashi da makami a wani fitaccen kantin saida kaya a Jihar ta Enugu.
Ya ce aikata fashi da makamin ya sabawa doka wanda ke karkashin sashe na 107(1)(b) na dokar soji Cap A20 LFN 2004, inda ya ce bisa sashe na 140 (3) na dokar sojoji, kotun ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru Goma a gidan na gyaran hali.
Janar Oluyemi Olatoye, ne ya kaddamar da kotun sojin a ranar 18 ga Fabrairu, 2025, domin yanke hukunci kan shari’o’in da suka shafi ma’aikatan da suka yi kuskure a cikin Rundunar.
A cewarsa, waɗannan hukunce-hukuncen sai sun samu tabbatarwa daga hukumomin soji da suka dace, wanda ya nuna ƙarshen shari’o’in sojojin.
Kanal Jonah ya kara da cewa Janar Oluyemi Olatoye ne ya kaddamar da kotun sojin tun a ranar 18 ga watan Fabrairun 2025, don yanke hukunci kan shari’o’in da suka shafi jami’an da suka yi ba daidai ba a cikin Rundunar.
Kazalika ya ce hukunce-hukuncen sai sun samu tantancewa daga hukumomin da suka dace, wanda hakan zai kawo ƙarshen shari’ar sojojin biyu.