Sarkin Kano na 16 Muhammad Sanusi ya gudanar da bikin nadin Gadaliman Kano Alhaji Munnir Sanusi Bayero da kuma sauran nade-nade da yayi a Masarautar a yau Juma’a.

Sauran sun hada da Alhaji Kabir Tijjani Hashim a matsayin Wamban Kano, da Alhaji Muhmud Ado Bayero a matsayin Turakin Kano, Alhaji Ahmad Abbas Sanusi a matsayin Yariman Kano, sai kuma Alhaji Adam Lamido Sanusi a matsayin Tafidan Kani.
A yayin bikin nadi Sarki Muhammad Sanusi na ll ya yi kira ga waɗanda aka nada da suka kasance masu yin shugabanci nagari da kiyaye kimar Masarautar da kuma jinkai ga al’umma.

Bikin naɗin ya samu halartar gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, shugabanin gargajiya da sauran manyan baki.

An gudanar da bikin nadin ne a fadar Sarkin da ke Kofar Kudu a yau.