Babbar jam’iyyar adawa a Najeriya PDP ta buƙaci al’ummar ƙasar da su farka a kan mulkin kama karya da ake yi a ƙasar.

 

A cewar PDP mulkin da jam’iyyar APC ke yi ba ta kan gwadaben demokradiyyar.

 

A don haka su ka bukaci al’umma da su yi amfani da ranar tunawa da demokradiyya a Najeriya wajen sake farkawa a kan yanayi da salon mulkin da jam’iyyar APC ke yi a Najeriya.

 

Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar Debo Ologunangba ne ya bayyana haka a sakon ranar demokradiyya ta Najeriya da su ka fitar.

 

A cewar sanarwar, akwai bukatar al’umma su farka wajen gane irin mulkin da ake yi a ƙasar.

 

Sun yi kira ga kungiyoyin fararen hula da masu ruwa da tsaki lan demokradiyya wajen hada kai da amfani da murya daya don kira da a yi adalci, gaskiya da kuma shirya sahihin zaɓe.

 

A cewar PDP mulkin da ake yi a ƙasar ya saba da kundin tsarin mulkin Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: