Rundunar yansandan jihar Katsina tayi nasarar cafke wani mutum mai suna Ibrahim Usman Mai shekaru 35, bisa zargin sa da sato wata mota Toyota kirar Coaster Bus.

Wanda ake zargin Ibrahim Dan jihar kano ne mazaunin Unguwar kwari a cikin Badawa, Wanda ya saci motan a bakin Ofishin Kamfanin sadarwa na G9 dake titin Audu Bako a Ranar Asabar.
Inda aka cafke shi a lokacin da yake yunkurin shiga kasar Nijar
Kakakin yansandan jihar Katsina SP Gambo Isah ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace sun cafke shi ne da mota kirar Toyota Coaster Bus Mai dauke da lamba AGL869R inda yanzu haka yana Hannun Rundunar yansandan don cigaba da bincike

