Kwamishinan Maaikatar Gidaje da Sufuri Barrister Musa Abdullahi Lawal ya bayyana shirin Gwamnatin Jihar Kano na ci gaba da samar da rukunin gidaje a farashi masu rahusa da yan Asalin Jihar zasu mallaka cikin sauki.

Kwamishinan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi ragamar aikin maaikatar sufuri da gidaje ta jihar Kano.
Ya tabbatar da cewar sake samar da rukunin gidaje a sassan jihar zai tallafa don magance matsalolin da karancin gidaje ke haifarwa a jihar, inda yace jihar kano tana bukatar sake gina rukunin gidaje duba da yadda jihar ke sake habaka ta fannin yawan alumma.

Kwamishinan maaikatar sufuri da gidaje ya kuma sake bayyana cewar gwamnatin Jihar kano za ta samar da ingantaccen shirin don tsabtace masu sana,ar babura masu kafa uku, yace gwamnati zata yi haka ne ta hanyoyin samar da ingantaccen tsari na yiwa masu baburan rijista domin yin duba akan ayyukansu da kuma zirga zirgarsu.

Ya kuma ce gwamnati zata Samar da tsarin zirga zirgar motocin haya na bai daya domin kamar yadda yake a sauran kasashen duniya da suka ci gaba
Barrister Musa Abdullahi Ya kuma yi kira ga maaikatan Hukumar da su mara masa baya domin samun nasarorin da yake fata tare da ciyar da gwamnatin jihar kano a fannin sufuri da gidaje.
Kwamishina Musa Abdullahi Ya kuma gargadi maaikatan maaikatar da su guji makara da fashi ba tare wani kwakwran uzuri ba.
Ya kuma hore su da su kauracewa sabawa dokokin maaikatan jihar