Atiku ya bayyana cigaba da tsare Nnamdi Kanu a matsayin zalunci tare da kira da a gaggauta sakin sa.

 

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana cewa cigaba da tsare jagoran ‘yan tada ƙayar baya na Biafra, Mazi Nnamdi Kanu, zalunci ne kuma cin zarafin doka. Atiku ya wallafa hakan ne a shafinsa na Facebook inda ya yi kira da a gaggauta sakin Kanu. Ya bayyana cewa ya gaza a matsayin sa na ‘ɗan ƙasa idan ya bari aka cigaba da tsare Kanu.

 

Nnamdi Kanu shi ne jagoran ƙungiyar tada ƙayar baya ta IPOB (Indigenous People of Biafra), wacce ta shahara da ayyukan ta’addanci. Haka kuma ana alaƙanta shi da ƙungiyoyin tada ƙayar baya kamar ESN (Eastern Security Network) da Biafra National Guard (BNG) waɗanda suka shahara wajen kashe-kashe da kai farmaki ga Hausawa da Fulani a yankin Kudu maso Gabas.

 

Tsawon shekaru, mabiyan Kanu sun yi sanadin mutuwar ɗaruruwan Hausawa, musamman direbobin manyan motoci, ɗalibai, ‘yan kasuwa da matafiya da suka rika cin karo da harin IPOB a hanyoyi da kasuwanni.

 

An kama Nnamdi Kanu a shekarar 2021 a ƙasar Kenya inda aka mika shi ga gwamnatin Najeriya ta hanyar ‘rendition’, wato Mika mutum mai laifi daga wata ƙasa zuwa wata ƙasa. Bayan haka aka gurfanar da shi gaban kotu bisa tuhume-tuhume masu nauyi, ciki har da cin amanar ƙasa (treasonable felony), tayar da fitina (incitement), da kuma taɗa ƙiyayya tsakanin kabilu (terrorism-related offences). Duk da wannan, Atiku ya fito a fili yana kiran a saki Kanu, abin da ya ƙara tayar da hankalin jama’ar Arewa waɗanda suka jima suna kallon Kanu a matsayin barazana ga rayuwarsu da zaman lafiyar ƙasar baki ɗaya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: